Dan takarar Gwamnan Jihar Jigawa a karkashin jam’iyyar LP, Abdullahi Tsoho, ya koma jam’iyyar APC mai mulki.

Hadimin Gwamnan Jihar, Badaru Abubakar, Habibu Nuhu Kila ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa ranar Juma’a.

Sanarwar ta ce dan takarar ya dauki matakin ne bayan ya fahimci APC na da dukkan muradun da ake bukata wajen ciyar da Jihar gaba.

Nuhu Kila ya kuma ce tsohon dan takarar ya sha alwashin cewa shi da dumbin magoya bayansa za su yi aiki tukuru wajen ganin APC ta yi nasara a zaben mai zuwa.

Yayin da yake karbarsa a ofishinsa, Gwamna Badaru ya nuna godiyarsa kan sauya shekar dan takarar, inda ya yi alkawarin cewa da shi da mutanensa za su ci gajiyar duk wani amfani da sauran ’yan jam’iyya ke ci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: