Yayin da ya rage saura kwanaki goma kacal a dakatar da karɓar kuɗaɗe da aka sauyawa fasali a Najeriya, kasuwanci na fuskantar barazana cikin waɗannan kwaanaki.

Gwamnatin tarayya ta sauya fasalin naira 200, 500 da kuma naira 1,000 tare da sanya wa’adin ƙarshen watan Janairun da mu ke ciki a matsayin ranar karshe da za a daina karɓar tsofaffin kuɗi.
A sakamakon hakan ya sanya wasu da dama daga cikin ƴan kasuwa musamman a Kano cibiyar Kasuwanci, su ka tsayar da ranar Laraba a matsayin ranar da za su rufe amsar tsofaffin kuɗin da aka sauya.

A ɓangaren ƙananan ƴan kasuwa kuwa sun sanya ranar Talata domin daina karɓar kuɗaɗen tare da ƙoƙarin shigar da waɗanda ke hannunsu zuwa gaba.

Wajen da gizo ke saƙar shi ne, har a yanzu babu wadatattun sabbin nairar a hannun mutane.
A wani bincike da Matashiya TV ta yi, ta gano wasu yankuna da ake sanya wani kaso kafin shigar da kuɗi ga masu sana ar POS.
Wata majiya taa tabbatar da cewar,ana karɓar naira 3,000 a matsayin caji idan mutum ya na so a tura masa naira 100,000.
Ko za a iya samun wadataccen kuɗin zuwa watan Fabrairu?
Tambayar da wasu mutaane ƴan Najeriya ke yi bayan ƙorafin rashin wadatar sabbin kuɗi a hannunsu.
Sai dai bankin Najeriya CBN ya ce ya kafa wani tsari da zai dinga karɓar tsofaffin kuɗin a mataki na ƙananan hukumomi na Najeriya.
Ko sabon tsarin na CBN ya fara aiki?
Har yanzu mutane na kokawa a dangane da batun sauyin kuɗin yayin da bankune ke cike don shigar da waɗand ake hannunsu zuwa asusun ajiya.
Ta yaya kasuwanci zai tsayaa cak a Najeriya?
Duba ga rashin wadatar sabbin kuɗin a hannun jama’a tare da ƙoƙarin mayar da tsofaffin zuwa bankuna, hada-hadar kasuwar na iya samun naƙasu duba ga yanayin da aka saba yin kasuwanci.
Da yawan ƴan kasuwa na amfani da takardar kuɗi wajen saye ko sayarwa a kasuwannin Najeriya.
Haka kuma mutane da ke siyayya na har yanzu akwai ƙaraancin kuɗaɗe a hannunsu yayin da ya rage saura kwanaki goma a dakatar da karɓar kuɗin a hukumance.
Ko za a iya samun sasdauci?
Akwai yuwuwar hakan duba ga cewa gwamnati ba ta yi aalbashi ba kuma ana kyautaa zaton biyan albashin da za a yi za a yi amfani da saabbin kuɗi qajen biya.