Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA sun kama wani makaho da kuturu dauke da tabar wiwi a Jihohin Kano da Osun.

Mai magana da yawun hukumar Femi baba Femi ne ya tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.

Baba Femi ya ce maahon da ake zargin da boye kayan mayen an kamashi ya boye a gidansa inda aka bashi kudi naira 6,000 a matsayin a jiya na watanni uku.

Sanarwarda Femi ya fitar ya bayyana sunayen mutanen da su ka hada da Aliyu Adebiyi wanda ya kasance makaho mai shekaru 67 inda aka samu kilogiram 234 a gidansa da Owena Ijasa da ke Jihar Osun.

Ya kara da cewa kuturun mai suna Haruna Abdullahi mai shekaru 45 an kamashi ne garin Garko da ke Kano a ranar Alhamis dauke da kilo giram 2.2 na tabar wiwi da kwayoyi.

Baba Femi ya ce hukumar ta kuma sake kama wasu mutane da su ke safarar miyagun kwayoyi a lokacin da su ke kokarin shigowa da hodar iblis bayan kunshe ta da su ka yi a cikin ganyen shayi da su ka shigo da ita daga kasasen ketare a tashoshin jirgin sama ta Enugu da Legas.

Leave a Reply

%d bloggers like this: