Abdulwahab wanda aka fi sani da Awarwasa ya kwanta dama a yau Litinin.

Matashin jarumin ya rasu bayan rashin lafiya da ya yi fama da shi.
Ɗan wasan Hausan ya rasu yayin da ake ci gaba da jimamin rasuwar Kamal Aboki da ya rasu sakamkon hatsarin mota daga Maiduguri zuwa Kano.
Awarwasa ɗan jihar Kano ya fito a finafinai da dama.

Daga cikin fina finan da ya fi shahara a ciki akwai A Duniya, shirin mai dogon zango.
