Shugaban kasa Muhammad Buhari ya kaddamar da manyanayyuka a Jihar Legas.

Shugaban ya kai ziyarar ne a ranar Litinin kuma ya kaddamar da tashar jirgin ruwa ta Lekki tare da ayyukan hadin gwiwa na gwamnatin Tarayya da gwamnatin Jihar.

Shugaban ya kuma kaddamar da wani kamfani mai zaman kansa mai suna Tolaram.

A ziyarar dai shugaban ya kai ya sake kaddamar da wani kamfanin shinkafa na ton 32 a kowacce sa’a daya wanda zai kasance daya daga cikin mafi girma a duniya.

Daga cikin ayyukan ciki harda cibiyar adana tarihi da kuma al’adun al’ummar Yarabawa.

 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bar Legas zuwa kasar Senegal a yau Talata inda zai halarci taron kasa da kasa na fannin noma karo na biyu.

 

Tawagar Shugaban ta kunshi Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama, Ministan Noma da Raya Karkara, Dr Mohammad Mahmood Abubakar, Mai ba Shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Mohammed Babagana Monguno, da babban darakta na hukumar Leken Asiri ta Kasa (NIA), Ambasada Ahmed Rufa’i Abubakar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: