Gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele, ya bayyana dalilin da yasa ba zasu dage wa’adin ranar daina amfani da tsaffin kudaden Naira ba.

Emefiele ya bayyana hakan yau Talata yayin hira da manema labarai biyo bayan zaman kwamitin kudi MPC a birnin tarayya Abuja.


Gwamnan ya jaddada cewa ranar 31 ga watan Junairu, 2023 ne ranar karshen amfani da tsaffin takardun kudin N500, N200 da N1000.
Emefiele ya ce ko shugaba Buhari ya amince kwanaki 100 da aka bada don mutane su canza kudadensu ya isa.
Ya bayyana cewa har dajin sambisa akwai kudi saboda sun tura jami’ansu su taimaka wajen canzawa mutane kudaden.