Babban Bankin Najeriya (CBN) ya karyata ‘yan Najeriya bisa cewa da suke ana fama da karancin sabbin kudade a bankunan dake fadin kasar.

Hakazalika, ya umarci ‘yan kasa da su gaggauta kai kudadensu banki domin a ajiye musu ko kuma a basu sabbi don gujewa asara yayin da wa’adi ke kara gabatowa.


Gwamnan CBN, Godwin Emefiele ne ya bayyana hakan ga manema labarai a birnin Jos, jihar Filato ta bakin daraktan fannin kula da biyan kudade na bakin, Musa Jimoh.
Ya bayyana cewa, sake fasalin da CBN ya yiwa Naira ya yi daidai da ka’ida da tafarkin duniya na sauya fasalin kudi duk bayan shekaru biyar, duk a Najeriya an shafe shekaru tara ba ayi sauyin ba.
Baya ga koken ‘yan Najeriya, majalisar wakilai ta kasa ta nemi CBN da ta duba yiwuwar kara wa’adin mayar da tsoffin kudaden kasar.
Da yake magana a yau Talata a lokacin taron wayar da kan jama’a game da sabbin kudi, daraktan ya nanata cewa, sake fasalin N200, N500 da N1,000 aiki na gwamnatin kasar nan don magance matsalolin yawaitar kudi a hannun jama’a.
Ya kuma bayyana cewa, wannan sauyin zai magance ajiyar kudade da ake yi ba a juya su a kasar tare da rage yawan kudaden bogi.