Jihar Katsina ta ayyana ranar Alhamis 26 da Juma’a 27 ga watan Janairun nan, a matsayin ranakun da ma’aikata za s huta, don yi wa shugaba Muhammadu Buhari maraba da zuwa jihar.

Gwamnatin jihar ta ce ta bayar da hutun ne, don shugabanni da wanda suke kananan hukumomin wajen Katsina shigowa don tarbar shugaba Buhari.

Wannan na kunshe cikin sanarwar da sakataren dindin na ma’aikatar kula da labarai da al’adu na jihar Alh Sani Bala Kabomo ya sanyawa hannu a yau Laraba.

Ana sa ran shugaba Buhari zai isa jihar Katsina don kaddamar da

wasu ayyukan raya kasa da gwamnatin jihar Katsina ta yi a karkashin gwamnan jihar Aminu Bello Masari.

Sanarwar da ta bayyana dalilin da shugaba Buharin zai kai ziyarci jihar tasa ta katsina a ranakun Alhamis da Juma’a din.

Sai dai hutun bai shafi ma’aikatan gwamnatin tarayya ba, bankuna da kuma ma’aikatun bayar da agajin gaggawa.

Ya ce suna kira ma’aikata da jam’ar gari da su fito kwansu da kwarkwatarsu, suyi dafifi dan tarbar shugaba buhari wanda zai je da yan tawagarsa bude ayyukan a jihar

Leave a Reply

%d bloggers like this: