Yan kasuwa a Birnin Kebbi sun yanke shawarar rufe kasuwa gaba daya saboda yadda karancin sabbin Naira ke hana su yin harkokinsu na yau da kullum.
Shugaban kungiyar ‘yan kasuwar jihar Kebbi, Alhaji Umar Dangura Gwadangwaji ne ya bayyana hakan.
A cewarsa, ‘yan kasuwa sun yi duk wani kokarin samun sabbin kudi daga bankunan kasar nan amma hakan ya gagara.
Da yake jawabi game da ci gaba da karbar tsoffin kudade, ya ce Idan suka ci gaba da karba daga hannun kwastomomi, babu bankin da zai karba daga wurinsu bayan karewar wa’adin.
A rahoton majiyar direbobi da masu sana’ar siyar da abinci a Birnin Kebbi sun daina karbar tsoffin kudade tun ranar Talata daga hannun kwastomomi.
Hakan ya faru ne saboda bankuna a birnin sun gaza ba da sabbin Naira da aka ce sun fara yawo tun watan jiya.
A cewar rahoton, mutane da yawa ne suka bi layin injin cirar kudi na ATM na tsawon awanni, amma sun gaza samun kudin cikin sauki ko rasa su ma kwata-kwata.