Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da kafa kwamitin mutum 14 da zai tabbatar an daina fama da wahalar fetur a Najeriya.

 

Daily Trust ta ce kwamitin zai dage wajen ganin an kuma saida fetur a kan farashin gwamnati, hakan yana zuwa ne a lokacin da ake wahalar samun mai a fadin kasar.

 

Buhari zai jagoranci kwamitin tare da karamin Ministansa na harkokin man fetur, Cif Timipre Sylva a matsayin wani shugaban.

 

Rahoton ya ce sauran ‘yan kwamitin sun hada da Ministar tattalin arziki, tsare-tsare da kasafin kudi, da Sakataren din-din-din na ma’aikatar harkar fetur.

 

A kwamitin akwai babban mai ba shugaban kasa shawara a harkar tattalin arziki, Shugaban hukumar DSS, shugabannin hukumomin kwastam da EFCC.

 

Sannan akwai shugaban hukumar NSCDC tare shugaban ma’aikatar NMDPRA da takwaransa na NNPC, da gwamnan babban bankin Najeriya na CBN.

 

Kwamitin zai yi aiki wajen duba yiwuwar gyaran matatun NNPC tare da bibiyar man da ake rabawa kullum domin sa ido a kan masu fita da shi zuwa ketare.

Leave a Reply

%d bloggers like this: