Dan takarar Shugabancin Najeriya a karkashin jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa, idan har ya samu nasara a zabe mai zuwa Gwamnatinsa za ta dukufa kan sauya fasalin Najeriya.

Atiku ya fadi Hakan ne a Jiya Alhamis, wajen gangamin yakin neman zabensa a filin wasa na Pa Ngele Oruta a Abakaliki.

Dan takarar ya bayyana cewa shi tuni yana goyon bayan sauya fasalin, kamar yadda jihohin kudancin kasar suke ta kira ga yin hakan.

Atikun ya kuma cewa, jam’iyyar PDP tana da abin da ake bukata dan sauya kasar nan, Dan haka jama’a su yi fitar dango su zabe ta.

Jaridar Blueprint ta ruwaito Atiku yana bukar masu zabe da su zabi PDP, tare da tabbatar musu da cewa Jam’iyyar APC ta ruguje.

Ya kuma bayyana cewa yana da zummar yi, dukkan jihohin kudanci suna ta kira a sauya fasali kuma yana tare dasu akan hakan.

A nasa bangaren Shugaban Jam’iyyar na kasa Iyorcha Ayu ya ce Jam’iyyar PDP ta kudurci ceto kasar nan, kuma a zata kawo karshen matsalar rashin tsaro da talauci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: