Tsohon shugaban Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo ya zargi shugabanni da jefa kasa a cikin hadari da barazana a dalilin son kan da suke yi.

 

Jaridar Punch ta rahoto Olusegun Obasanjo yana mai kokawa da cewa ana rabon mukaman gwamnati ba tare da an yi adalci ba, ya na zargin ana nuna son kai.

 

Obasanjo ya tuhumi Gwamnatin Muhammadu Buhari da zaben na kusa da ita ta na daura su a kujerun gwamnati, a maimakon ayi la’akari da cancanta.

 

Tsohon shugaban kasar ya yi wannan bayani da ya ke gabatar da jawabinsa kan muhimmancin makarantun gwamnati wajen kawo hadin-kai a Najeriya.

 

Rahoton ya ce Obasanjo ya gabatar da jawabi ne a makarantar sakataren gwamnatin tarayya da ke Kaduna a wajen bikin makarantar shekaru 50 da kafuwa.

 

A maimakon a rika tafiya da kowa a wajen yin rabon kujeru da mukamai, Obasanjo ya ce gwamnatoci, ‘yan siyasa da jam’iyyu wasu abubuwan suke kallo.

 

Da yake bayani a garin Kaduna, tsohon shugaban na Najeriya ya koka a game da tattalin arziki, ya ce talauci ya karu, farashin kaya sun tashi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: