Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Litinin yayi kira ga ‘yan Najeriya da su gode kan halin da suke ciki a kasar nan idan suka duba yadda wasu kasashe suke.

 

Shugaban kasan ya bayyana hakan ne a dakin taron Banquet na Kano bayan kammala ziyarar da ya kai ta kaddamar da ayyuka a jihar.

 

Kamar yadda Femi Adesina, hadimin shugaban kasan ya sanar a wata takarda, Buhari ya kwatanta cigaba a ababen more rayuwa a fadin kasar nan matsayin abun alheri.

 

Ya ce suna da gagarumar kasa amma ba sa godewa har sai sun ziyarci kasashen da suke makwabtaka da su inda jama’a ke cin abinci sau daya a rana.

 

Ya ce, a yayin da yake helikwafta, yawan manyan gine-ginen da ya gani da yawan cigaba da ya hango a kasa abun farin ciki ne. Sun godewa Allah.

 

Channels TV ta rahoto cewa, Buhari yayi kira ga masu kudi da su karfafawa matasa guiwa inda yace ko sun so, ko sun ki sai sun bar musu kasar.

 

Ya taya Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano murna kan ayyukan da yayi a bangaren more rayuwa inda ya kara da cewa ziyarar da ya kai baya-bayan nan a Kogi, Yobe, Legas da Katsina sun nuna cewa gwamnonin sun yi kokari da iyakar iyawarsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: