Hukumar yaki da aikata miyagun laifuka ta Birtaniya NCA ta bayyana cewa wasu wasiku biyu da ake yadawa a shafukan sada zumunta wanda su ke nuna da hukumar na zargar ‘yan takarar shugaba kasa a Najeriya da jam’iyyun siyasar kasar da aikata ba daidai ba.

 

Hukumar ta ce dubban mutane ne su ka karanta wasikar na bogi a shafukan sada zumunta na Twitter wanda aka bayyana cewa hukumar ce ta wallafa.

 

Hukumar ta ce wasikar da aka wallafa ta an wallafa ta ne a karshen watan janairun da ya kare wanda wasikar ta ke nuni da hukumar na zargin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Asiwaju Bola Ahmad Tinubu akan aikata almundahana.

 

Hukumar ta kuma bayyana cewa wasika ta biyu an wallaafa cewa hukumar tana binciken jam’iyyar hamayya ta Labour da zargin rubuta wasikar farko.

 

Inda ta ce dukkan wasikun da aka wallafa ba gaskiya ba ce.

Leave a Reply

%d bloggers like this: