Wasu da ake zargi ‘yan bindiga ne sun harbe wani Alkali kuma shugaban Kotun Kostomaren Ejemekwuru Nnaemeka Ugboma a ranar Alhamis.

 

Lamarin ya farune a karamar hukumar Oguta ta Jihar Imo.

 

Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa ‘yan bindiga sun je kotun ne akan babura tare da kutsa kai ciki, kuma bayan shigar su cikin kotun su ka fito da Alkalin a lokacin da ya ke tsaka da yanke hukuncin shari’ar da ya ke gudanarwa.

 

Shaidan ya ce bayan fito da shi su ka hallaka shi inda su ka hau baburan su su ka tsere.

 

Alkalin da maharan su ka hallaka ya kasance dan Asalin Nnebukwu a karamar hukumar ta Oguta ta Jihar.

 

Wani ɗan uwa ga Alkalin ya tabbatar da kisan inda ya bayyana cewa bayan kisan dan uwan sun shiga cikin mummunan hali.

 

Shima a nasa bangaren shugaban kungiyar lauyoyi ta Najeriya shiyyar Owerri Ugochukwu ya tabbatar da faruwar lamarin .

 

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Henry Okoye ya ce kisan da maharan su ka yi akwai ban tausayi a cikin sa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: