Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta tabbatar da cewar ta kammala shirinta staf domin domin gudanar da zaɓen shekarar 2023 da mu ke ciki.

Shugaban hukumar Farfesa Mahmu                  d Yakubu ne ya tabbatar da haka yayin  gwajin sabuwar  na’urar tantance masu kaɗa ƙuri’a da akaza a yi amfani da ita.

An yi gwajin na’urar tantancewa a mazaɓu 436 na jihohi 36 na Najeriya.

Shugaban hukumar wanda ya ziyarci wasu mazaɓu da ke babban birnin tarayya Abuja, ya ce sun gamsu da aikin na’urar wanda ya ƙara musu ƙarfin gwiwar tunkarar zaɓen.

Ya ƙara da cewa daga sauran bayanai das u ka samu daga sauran jihohi dukka sun samu nasarar gudanar da gwajin cikin daƙiƙa talatin a kowanne mutum.

Hukumar ta gudanar da ssabbin tsare-tsare domin tunkarar babban zaɓen shekarar 223 da mu ke ciki wanda aza a fara daga ƙarshen watan da mu ke ciki.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: