Gwamna Muhammad Badaru Abubakar na na jihar Jigawa ya amince da nadin Muhammad Hameem a matsayin sabon sarkin Dutse.

Muhammad Hameem ya gaji Sarki Nuhu Muhammad Sunusi, wanda ya kwanta dama a makon jiya a wani asibitin Abuja.


Manema labarai sun tattaro cewa masu nada sarki a masarautar Dutse sun hada kai sun zabi sabon sarkin cikin masu takarar kujerar sarautar guda uku.
Wata sanarwa daga majalisar masarautar ta ce an mika sunan sabon sarkin majalisar sarakunan jihar Jigawa wacce ita ma ta amince da hukuncin masu nada sarkin.
Bayan nan majalisar sarakunan ta mika sunayen Muhammad Hameem da sauran yan takarar biyu ga gwamnan jihar don samun yardarsa.
Idan za ku tuna, a ranar Laraba, 1 ga watan Fabrairu ne aka yi jana’izar mariyi sarkin Dutse, Alhaji Nuhu Muhammad Sanusi, inda aka sada shi da gidansa na gaskiya.
Taron jana’izar marigayin ya samu halartan manyan sarakunan Arewa ,manyan yan siyasar Najeriya, manyan malaman addini da kuma yan’uwa da abokan arziki.