Kotun tarayya da ke zamanta a babban birnin tarayya Abuja ta umarci Babban Bankin Najeriya (CBN) da kada ya kunce damararsa game da wa’adin daina amfani da tsoffin Naira.

 

Wannan na zuwa ne a cikin wani hukuncin da aka yanke a ranar Litinin 6 Faburairu, 2023 kan kara mai lamba FCT/HC/CV/2234/2023 da aka shigar a gaban kotun.

 

CBN, Buhari da sauran bankunan kasar nan ne aka sanya a matsayin wadanda ake kara a cikin takardar da aka kai gaban alkali.

 

Mai shari’a Eleojo Enenche na kotun FCT ya umarci CBN da kada ya tsawaita wa’adin 10 ga watan Fabrairu nan da zuwa lokacin da kotu za ta sake duba karar.

 

A hukuncin, alkali ya ce kada CBN ya kuskura ko shi ko ma’aikatansa su dago batun tsawaita wa’adin daina amfani da tsoffin N200, N500 da N1000.

 

Hakazalika, kotun ya ce, ya zuwa lokacin da za a saurari karar, 10 ga watan Fabrairu ne wa’adin karshe na daina amfani da tsoffin kudade.

 

Wannan umarni na kotu zai yi amfani ne na tsawon kwanaki bakwai har zuwa lokacin da za a saurari batun a ranar 14 ga watan Fabrairu.

 

Wadanda suka shigar da karar sune jam’iyyun Action Alliance (AA), Action Peoples Party (APP), Allied Peoples Movement (APM), da kuma kungiyar siyasa ta National Rescue Movement (NRM).

Leave a Reply

%d bloggers like this: