An rufe bankuna a Abeokuta babban birnin jihar Ogun sakamakon zanga-zanga da wasu matasa su ka yi sanadin karancin sabbin kudi a hannun jama’a.

Masu zanga-zangar sun balle allunan talan yan siyasa da kuma kone-kone a wasu hanyoyi na garin.
An rufe wasu bankuna musamman na yankin Oke-Iewo don gudun kada fusatattun matsan su bakawai ma’aikata.

Rahotanni daga jihar sun ce an kona wani banki a jihar tare da rushe wasu wani banki.

Ko a ranar Litinin sai da gwamnan jihar ya ziyarci bankin Najeriya CBN reshen jihar a kan karancin sabbin kudade.
Mutane na shafe awanni a injinnan cirar kudi na ATM tun bayan da aka kara wa’adin daina karbar tsofaffin kudin wanda lokacin lamatsalar ta kara ta’azzara.