Babban bankin Najeriya CBN ya tabbatarwa da hukumar zabe a Najeriya INEC cewar ba za ta yi silar kawo cikas a babban zaben da ake tunkara ba.

Gwamnan bankin Gdwin Emefiele ne ya tabbatar da wannan yayin da ya ke karbar ziyarar shugaban hukumar zabe na kasa da wasu manyan ma’aikatar.

Shugaban hukumar Farfesa Mahmud Yakubu ya ce sn je ne domin samun tabbaci dangane da sabon kudi da banin ya fiar da kuma dokar takaita cirar kudi daga asusun a jiya na banki a kullum.

Farfesa Mahmud Yakubu ya bayyana alfanun da ke tattare da tsariin sauya fasain kudi da takaita cirarsa a kullum.

Hukumar zabe ta INEC ta karfafi babban bankin Najeriya CBN a kan matakin da ya ke tare da kara goyn bayan bankin.

Gwamnan bankin Godwin Emefiele ya tabbatar da cewar bankin ba zai zama cikas ga babban zaben da ake tunkara ba.

Sannan ya ce zai tabbatar ba a samu guda cikin ma’aikatan bankin daga cikin masu marawa wata jam’iyya baya ba a ranar zabe.

Leave a Reply

%d bloggers like this: