Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya sa labule da shugaban ƙumgiyar gwamnonin Najeriya, Aminu Tambuwal da shugaban gwamnonin APC, Atiku Bagudu.

Channels TV ta rahoto cewa shugaban ƙasan ya zauna da manyan gwamnonin ne kan halin da ake ciki na karancin sabbin takardun naira guda uku da CBN ya canja.


Sauran manyan jiga-jigan da suka halarci zaman sun haɗa da, gwamnan babban banki CBN, Godwin Emefiele, shugaban hukumar yaƙi da cin hanci (EFCC), Abdulrasheed Bawa.
Haka zalika shugaban dakarun tsaron ƙasar nan, Janar Lucky Irabor, ya halarci taron wanda ya gudana a ofishin shugaban kasa da ke Aso Villa a birnin tarayya Abuja.
Kasancewar gwamnan babban bankin na CBN, ya nuna cewa an shirya taron ne bisa ka’ida domin tattaunawa kan manufar musanya kudi da aka kwashe kwanaki ana ta cece-kuce da jama’a, musamman daga gwamnonin.
Idan dai ba a manta ba a ranar 3 ga watan Fabrairu ne shugaban kasar ya gana da gwamnonin jam’iyyar APC inda wasu daga cikin gwamnonin suka bukaci shugaban kasar ya sa baki domin ba da dama ga tsofaffi da sabbin takardun kudi a hade domin a samu saukin cuwa-cuwa. a fadin kasar.
An ce shugaban kasar ya soke shi ne duba da umarnin kotu na hana gwamnati kara wa’adin ranar 10 ga watan Fabrairun 2023 na musanya tsofaffin takardun naira uku.
Sai dai babu daya daga cikin mahalarta taron da ya amince ya yi magana da manema labarai.