Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta dakatar da gwamnatiin tarayya da babban bankin Najeriya CBN daga kara wa’adin daina karbar tsofaffin kudin da aka sauyawa fasali.

Kotun ta tsayar da ranar 1 ga watan Fabraiiru da mu ke ciki a matsayin ranar karshe da za a daina amfani da da tsofaffin kudin da aka sauya na naira 2, da kuma naira 1,000.

Yayin da ya ke karanto hukuncin, mai shari’a Eeojo Enenche ya dakatar da bankin Najeriya CBN da gwamnatiin Tarayya kan kara wa’adin daga ranar 10 ga watan Fabrairu da mu ke cikI.

Kotun ta ayyana ranar 14 ga watan Fabrairun da m ke ciki a matsayin ranar da za ta ci gaba da sauraron karar.

Wasu jam’iyyun siyasa a Najeriya kamar AA, APP APM da jam’iyyar NMR ne s ka shigar da karar a gaban kotun tare da bukatar dakatar da yunkurin bankin da kuma gwamnatin tarayya na kara wa’adin.

A bangare guda kuma wasu gwamnonin jam’iyyar APC sun shigar da karar gwamnatin tarayya da babban bankin Najerya a kan wa’adin da aka saka da kuma mafi karancin kudi da mutane za su iya fitarwa daga asusunsu a kullum.

A farko gwamnatin tarayya ta saka ranar 31 ga watan Janairu a matsayin ranar karshe da za a daina karbar tsofaffin kudi, sai dai gwamnatin da babban bankin Najeriya CBN sn kara wa’adin daga ranar 31 ga Janairu zuwa 17 ga watan Fabrairu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: