Kamfanin BUA ya kaddamar da aikin fadada hanyar Kano zuwa Kazaure zuwa Kongolam mai tsawon kilomita 132 tare da hadin gwiwar ma’aikatar ayyuka da gidaje ta tarayya.

Wannan matakin ya yi daidai da dokar zartarwa ta shugaban kasa mai lamba 007 kan bunkasa ababen more rayuwa da tsarin bada harajin zuba jari na gyaran hanya, wanda ya ba da izinin cire haraji ga wasu gungun ‘yan asalin kasar don gudanar da gyaran manyan titunan gwamnatin tarayya.
Ministan ayyuka da gidaje Babatunde Raji Fashola ne ya kaddamar da aikin na Naira biliyan 116 a wani biki a Kazaure ta jihar Jigawa.

Sanarwar da kamfanin BUA ta fitar ta ce, aikin zai ratsa jihohin Kano, Jigawa, da Katsina daga zagayen Dawanau a jihar Kano zuwa Kongolam a jihar Katsina.

Ministan, a cewar sanarwar, ya bayyana cewa kamfanin BUA Group ne zai kasance mai kudin aikin na biyu na aikin gina hanyar mai tsawon kilomita 132 a wani bangare na ci gaba da ayyukan raya ababen more rayuwa.
Da yake jawabi a wajen bikin, Babban Daraktan Rukunin na BUA, Kabiru Rabiu, ya ce BUA ta ci gaba da jajircewa wajen hada kai da gwamnati kan muhimman ayyuka da tsare-tsare da za su hanzarta samar da ci gaban bil’adama, zamantakewa, da samar da ababen more rayuwa a fadin kasar nan.
Rabiu ya ce kamfanin BUA wadda shi ne ke ba da kudin aikin kuma ya riga ya tattara kayan aiki zuwa wurin kuma ya na da iya aiki, gwaninta, da kayan aiki don kammala hanyar a kan jadawalin.
Ya kuma mika godiyarsa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ministan ayyuka da gidaje bisa amincewa da aikin tare da jaddada kudirin kungiyar na samar da hanyar mota guda biyu wadda za ta kasance cikin mafi inganci a nahiyar Afirka.
Fashola ya ce babbar hanyar, wadda kamfanin BUA Group ke ginawa tare da sauran kayayyakin more rayuwa, zai karama ayyukan gina layin dogo da gwamnatin tarayya ke gudanarwa a shiyyar Arewa maso Yamma a Najeriya, sannan kuma za ta kara bude hanyoyin tattalin arziki ga Najeriya da yankin yammacin Afirka.