Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kira wani taron gaggawa na majalisar kolin shugabannin Najeriya wanda zai gudana a ranar Juma’a, mai zuwa.

Shugaba Muhammadu Buhari da sauran manya za su zauna ne a kan halin da kasa ta ke ciki.

Makasudin zaman shi ne rigingimun da ya barke a wasu yankuna a dalilin sauyin takardun kudi da kuma wahalar man fetur da ake ta fama da shi.

Zaman da za ayi a fadar shugaban kasa zai tabo sha’anin rashin tsaro da shirye-shiryen zaben 2023.

Za a fara taron da karfe 10:00 na safiyar ranar.

Rahoton ya tabbatar da cewa ana sa ran Gwamnan babban banki na kasa Godwin Emefiele zai yi wa majalisar bayani kan tsarin canjin kudin.

Wata majiya ta ce shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu da Sufetan ‘Yan sanda na kasa, Usman Alkali Baba za su yi magana a taron.

Majalisar za ta ji inda aka dosa a kan shirye-shiryen da hukumar zabe da jami’an ‘yan sanda suke yi, ganin saura kwanaki 17 ayi babban zabe.

A wajen zaman ne ake sa ran gwamnatin tarayya za ta dauki muhimman matakai a kan sha’anin zabe mai zuwa da kuma canjin takardun Naira.

Leave a Reply

%d bloggers like this: