Shugaban kasa Muhammad Buhari ya jagoranci taron Majalisar Koli ta kasa domin tattauna manyan batutuwa da su ka addabi Najeriya.

 

Taron wanda aka gudanar a fadar shugaban da ke Abuja a yau Juma’a ,inda aka tattauna akan matsalar sauyin kudi karancin takardun naira, matsalar man fetur da kuma sha’anin tsaro sakamakon gabatowar babban zaben shekarar da muke ciki.

 

Taron wanda ya samu halattar tsofaffin shugabannin Najeriya da su ka hada da Abdulsalamu Abubakar, Yakubu Gawon, Goodluck Jonathan, Olusegun Obasanjo da gwamnonin Jihohi da kuma shugabannin majalisar dokoki na kasa.

 

A yayin zaman ciki harda gwamnan babban bankin Najeriya CBN Shugaban hukumar zabe INEC shugaban hafsan tsaro shugaban hafsan sojin kasa shugaban hukumar ‘yan sanda na Kasa da kuma kwamandan NSCDC.

 

Sauran sun hada da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbanjo Sakataren gwamnatin tarayya shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya da sauran manyan jami’an gwamnati.

Leave a Reply

%d bloggers like this: