Gwamnatin Jihar Kano ta kai gwamnatin tarayya kara kotun koli kan sauyin fasalin kudi.

Karar wadda babban lauyan Jihar ya shigar ta hannun lauyansa Sunusi Musa ya bukaci kotun koli ta ayyana cewa shugaban kasa Muhammad Buhari shi kadai bashi da hurumin bai’wa babban bankin kasa na CBN izinin dakatar da daina amfani da naira tsofaffin kudi na naira 1000 500 da kuma naira 200 ba tare da amincewar majalisar tattalin arziki da majalisar zartarwa ta kasa ba.


A cikin karar da gwamnatin ta shigar ta bukaci kotun ta ayyana cewa akwai bukatar shugaban ya tattauna da majalisar zartarwa ta kasa da kwamitin tattalin arziki na kasa kafin daukar matakin hakan.
A cikin takardar karar da aka shigar gaban kotun ta bayar da umarnin tilastawa gwamnatin ta tarayya ta janye tsarin hana amfani da tsohon kudin.
Takardar ta nuna yadda tsarin ya kawo cikas ga tattalin arziki da kuma al’umma sama da miliyan 20 da ke zaune a Jihar.
Jihar na son kotun ta tilastawa gwamnatin ta tarayya janye tsarin sauya fasalin naira,inda ta ce tsarin ya ci karo da tanadin kudin tsarin mulkin kasa na shekarar 1999 da aka yiwa kwaskwarima.
Sannan kotun ta dakatar da umarnin da shugaban ya baiwa CBN na takaita cirar kudi a kowacce rana daga asusun ajiya wanda hakan ya sabawa tsarin mulki tare da sabawa doka.