Bayan kammala taron majalisar Kolin Najeriya mahalatta taron sun nuna goyon bayan su ga gwamnatin tarayya akan sauyin fasalin kudin da babban bankin kasa na CBN ya yi.

Majalisar ta bayyana cewa ta goyi bayan sauyin ne tare da sharadin bankin ya gaggauta ganin cewa ‘yan Najeriya sun wadatu da sabbin kudaden.

Majakisar ta kuma bukaci gwamnan babban bankin Godwin Emefiele da ya samar da wadatattun sabbin kudaden ko kuma ya fitar da tsofaffin al’umma su yi amfani da su.

Ministan Shari’a na Najeriya Abubakar Malami SAN tare da gwamnan Jihar Legas Babajide Sanwoolu da gwamnan Jihar Taraba Darius Ishaku su ne ka shedawa manema labaran fadar shugaban kasa.

Abubakar Malami ya ce abubuwa guda biyu aka tattauna akan su a gurin zaman, inda aka tattauna akan zaben shekarar da muke ciki da kuma sauyin fasalin kudin kasar.

Malami ya ce shugaban hukumar hukumar zabe ta kasa INEC Farfesa Mahmud Yakubu da shugaban ‘yan sanda na Kasa Usman Baba Alkali IGP sun bayyana cewa sun shirya tsaf domin gudanar da zaben.

Ya kara cewa a ɓangare kudi kuma an bukaci CBN da ya tabbatar da ya buga wadatattun kudaden da za su wadatar da ‘yan Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: