Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana cewa ya zama wajibi malaman jami’o’i na kasa da za su aikin turawan zabe su yi rantsuwa kan cewa ba za su nuna banbanci a lokacin tattara sakamakon zabe ba.

Shugaban hukumar na kasa Farfesa Muhmud Yakub ne ya tabbatar da hakan a wajen taron da yayi da shugabanni jami’o’i a ranar Alhamis.


Shugaban ya ce rantsuwar zata kasance ne akan kowanne ma’aikacin zabe kamar yadda sashe na 26 na kudin zaben shekarar 2022 ya tanada.
Daily Trust ta rawaito cewa Muhmud Yakub ya ce dukkan malamin jami’ar da alakarsa da wani dan siyasa ta fito fili hukumar ba za ta yi aiki dashi ba.
Yakub ya kara da cewa dukkan wani ma’aikaci da ke harkar siyasa ko ya ke alaka da ‘yan siyasa ko kuma aka taba kamashi da badakatar zabe hukumar ba za ta yi aiki dashi ba.
A yayin jawabin shugaban hukumar jami’o’i ta Kasa NUC Farfesa Abubakar Rasheed yayi kira ga malaman jami’o’in da za su tura aikin zabe su zamo kwararru domin ganin sun sauke nauyin da aka dora musu.