Gwaman babban bankin Najeriya Godwin Emefiele ya sanar da abinda ya hana wadatuwar sabbin kudade a Najeriya.

Emefiele ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a gurin taron majalisar Kolin Kasar kan sauyin fasalin kudin kasar.
Gwamnan ya ce a halin yanzu babban bankin na CBN ba shi da halin buga sabbin takardun kudin da za su wadatar da ‘yan Najeriya sakamakon yankewar takardun da ake buga kudin.

A yayin zaman wata majiya daga Premiun Times da ta halacci gurin zaman na majalisar kolin ta rawaito cewa Gwamnan bankin Emefiele ya nuna rashin jin dadinsa dangane da yankewar takardun da ake buga kudin tare da kawowa tsarin tsaiko.

Gwamnan ya bayyanawa majalisar cewa kamfanin da ya ke aikin buga kudin na Kasa wato Najeriya Security Printing and Minting PLC ya gamu da cikas din ne rashin buga takardun kudin wanda hakan ya hana wadatuwar sabbib kudin.
Emefiele ya kara da cewa ya zuwa yanzu babban bankin ya bayar da umarnin kawo takardun buga kudin daga wani kamfani a kasar Jamus da Birtaniya amma har kawo yanzu ba a kawo takardun ba.
Gwamna Emefiele ya ce sun mika wa kamfanin buga kudin bukatar buga sabbin kudin naira miliyan 70 wanda karin zai sanya a samu karin naira biliyan 126 zuwa jiya Juma’a wanda hakan zai wadatar da al’umma amma hakan ya gaza samuwa sakamakon karewar takardun da ake buga kudin.