Daraktan yada labaran kwamitin yakin neman zaɓen dan takarar shugaban kasa a Jam’iyyar APC Me Bayo Onanugu ya soki wasu manyan jami’an gwamnati kan sauyin fasalin kudin kasar

Daraktan ya shaida hakan ne ta cikin wani gajeren bayani da yayi a shafinsa na Twitta, inda ya soki bukatar da Malami ya shigar gaban kotun Koli bayan hukuncin da kotun ta yanke.
Onanugu ya bayyana cewa ministan Shari’a Abubakar Malami SAN da gwamnan babban bankin kasa CBN Godwin Emefiele ba sa kaunar ‘yan Najeriya.

Mr Bayo ya ce ya zuwa yanzu sun gane Malami baya kauna Najeriya da Mutanen da ke cikin ta.

Ya kara da cewa ba sa goyon bayan kudurin na Ministan shari’ar kan sauyin kudin.