Gwamnan Jihar Zamfara Muhammad Bello Matawalle ya bayar da umarnin kama dukkan wanda yaki amsar naira 1000, 500, 200 na tsohon kudi.
Gwamna Matawalle ya tabbatar da hakan ne a gurin bikin rantsar da manyan Alkalai tare da sabbin nade-naden hadimai wanda aka gudanar a gidan gwamnatin Jihar da ke Chamber ll Garin Gusau babban birnin Jihar.
Matawalle ya bayyana cewa tsofaffin takardun kudaden har yanzu akwai halaccin amsar su har zuwa ranar da Kotun Koli za ta yanke hukuncin karshe da gwamnonin Jihohi uku su ka shigar da gwamnatin tarayya.
Gwamna Matawalle ya ce sauyin kudin ya haifar da halin kakani kayi ga tattalin arzikin kasa sanadin yunkurin sauyin kudin da babban bankin yayi na haramta amfani da tsohon kudin a ranar 10 ga watan Fabrairu da muke ciki.
Matawalle ya ce sauyin kudin ya kara kawo nakasu ga Jihar wadda ta ke fama da matsalar ‘yan bindiga da masu aikata manyan laifuka wanda hakan ya kawo taɓarɓarewar tattalin arzikin Jihar da sauran makwabtan Jihar.
Muhammad Bello Matawalle ya yaba da hukuncin da kotun koli ta dauka na dakatar da yunkurin na CBN wanda hakan ya ragewa mutane wahalhalu a halin da su ka shiga.