Kungiyar mayakan ISWAP ta hallaka wani kwamandan boko haram mai suna Abu Zarah da wasu mayakansa 15 a Jihar Borno.

 

Lamarin ya farune bayan wani kazamin fada da su ka yi a tsakanin su.

 

Masanin tsaro Zogazola Makama da ke yankin tafkin Kasar Chadi ya tabbatar da cewa mayakan na ISWAP karkashin jagorancin Ba’ana Chingori ne su ka kaiwa mayakan na boko haram hari a kauyen Gulmare da ke cikin karamar hukumar Konduga a Jihar Borno.

 

Wata majiya daga Jihar ta bayyana cewa rikicin ya faru bayan wani hari da aka kaiwa sabon Amir Jaysh na kungiyar boko Haram Alhaji Ali Hajja Fasam.

 

Ali Hajja wanda ya dawo daga sansanin Ali Ngulde da ke tsandaurin Mandara inda ya amso makamai da babura takwas.

 

A harin da aka kai musu Ali Hajja ya tsere inda ya bar wata babbar bindiga.

Leave a Reply

%d bloggers like this: