Rundunar ‘yan sandan Jihar Anambra ta tabbatar da mutuwar jami’anta wanda wasu ‘yan bindiga su ka yi a garin Ihiala da ke karamar hukumar ta Ihiala a Jihar.

Mai magana da yawun runduar ‘yan sandan Jihar DSP Tochukwu Ikenga ne ya tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar yau Asabar, inda ya ce lamarin ya faru ne a jiya Juma’a.

Kakakin ya ce maharan sun kai harin ne da misalin karfe 2:40 na rana, inda jami’an ‘yan sandan yankin su ka samu kiran gaggawa kuma su ka kai dauki akan hanyar Isheka Ihiala su ka dauko gawarwakin jami’an yan sanda uku wasu kuma su ka jikkata.

Ikenga ya ce jami’an da su ka rasa rayukan su su na aiki ne a sashen kula da abubuwan fashewa EOD na rundunar ‘yan sandan Jihar Delta.

Jami’in ya ce ‘yan sada uku da aka hallaka su na kan hanyar su ne ta zuwa Jihar Abia a yankin Ihiala.

Ya ce bayan harin sun aike da jami’an su gurin domin binciko ‘yan bindigan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: