Babban bankin Najeriya (CBN) ka iya sake fitar da ƙarin takardun sabbin kuɗi zuwa hannun al’umma ta bankunan kasuwanci yau Litinin, 13 ga watan Fabrairu, 2023.

A rahoton da jaridar The Nation ta haɗa, kusan biliyan 500 na sabbin takardun da aka sauya wa fasali ne aka fitar kuma mutane ke hada-hada da su tun daga watan Disamba, 2022.
Wani mamban majalisar gudanarwan CBN, wanda ya yi jawabi da sharaɗin boye bayanansa, yace bankin zai rabawa bankuna kusan Tiriliyan ɗaya a yau Litinin.

Sanarwar jami’in babban bankin ta ce CBN zai yi duk abinda ake bukata domin tabbatar da ya kawar da ƙuncin rayuwar da ‘yan Najeriya suka tsinci kansu.

Wannan sabon motsi da babban bankin ya yi ka iya zarce tunanin wasu gwamnoni a Najeriya, waɗanda suka yi ikirarin gwamnan CBN na da wata boyayyar manufa a lamarin.
A cewar gwamnonin ciki harda na Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai, Godwin Emefiele, na da wata manufa a ɓoye saboda bai tashi kawo tsarin ba sai a kakar zaɓe.
Akalla gwamnatocin jihohi Bakwai ne suka shiga Kotu suna kalubalantar sabon tsarin da gwamnatin tarayya ta kawo, sun ƙara da cewa lamarin ya jefa da yawan yan Najeriya cikin ƙunci.