Shugaban kasa Mahammadu Buhari ya hallaci hukumar yan sanda ta kasa yau litinin domin kaddamar da wasu kayayyakin aiki da hukumar yan sanda za ta fara amfani da su.

Kamar yadda sanarwa ta fito daga mai taimakawa shugaba Buhari a kan kafafen yaɗa labarai Femi Adesina, ya ce shugaba Buhari zai bude abubuwa da Jami an za su samu Saukin yin aiki yadda yadda dace.
Kayyayakin aiki wadanda suka hada da motocin da bindigu da riguna masu silke da sauran wasu kayyaki.

Sannan shugaban kasa mahammadu Buhari ya nemi rundunar yan sanda ta yi iya kokarinta domin tabbatar da an gundanar da zabe cikin kwanciyar hankali ba tare da an samu wata matsala ba a yayin gudanarwa.

Sai dai a wani rahoto da yake bayyana ya nuna an Kai hari ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa wato INEC sama da 300.
Shugaba Buhari ya samu yan rakiya da su ka haɗa da ministoci da sauran mukarraban gwamnati.