Gwamnan babban bankin Najeriya CBN Godwin Emefiele yace dokar daina karɓar kuɗi a Najeriya tana nan daga ranar 10 ga watan Fabrairu daya gabata.

Gwamnan ya sake jaddada haka ne yau yayin daya ziyarci ma’aikatar ƙasashen waje domin tattauna batun sauya fasalin wau takardun kuɗin ƙsar.


Ya ce babu wani abin duba dangane da ƙara wa’adin karɓar wanda kotun ƙoli ta yi.
Ya sake jaddada cewar dokar daina karɓar kuɗi tana nan wanda hakan ya sa wasu bankunan ƴan kasuwa ba sa karɓar tsofaffin kuɗi.
Emefiele ya sake jaddada cewar babu buƙatar tsawaita lokacin daina karɓar kuɗin daga ranar 10 ga watan Fabrairu.
Ko a makon da ya gabata sai da dattawan Najeriya su ka zauna a fadar shugaban ƙsa domin duba dokar har su ka gamsu tare da goyon bayan hakan.
Sai dai wasu gwamnoni a Najeriya na ci gaba da shigar da ƙara gaban kotu tare da ƙalubalantar tsarin wanda su ka ce wa’adin da aka saka ya yi kaɗan.