Gwamnatin jihar Zamfara ta umarci dukkanin ƙungiyoyi masu zaman kansu a jihar su dakatar sannan su fice daga jihar.

Hakan na ƙunshe a wata sanarwa da kwamishinan tsaro da al’amurancikin gida MammanTsafe yafitar.

Gwamnatin ta yi zargin yadda ƙungoyoyin ke yin ayyukan da su ka saɓawa doka a jihar.

Sanarwar ta ce mafi yawa daga cikin ƙungiyoyin basu yi rijista da gwamnatin jihar ba kafon su fara ayyukansu.

Gwamatin ta yi zargin ayyukan ƙungiyoyin da rura wutar matsalar tsaro a joihohin da ke maƙobtaka da Zamfara.

A cikin sanarwar, gwamnatin ta yi gargaɗi ga hukumomingwamnatin das u ka yi aiki da duk wata ƙungiya dab a tad a rijista.

Kuma an bai wa jami’an tsaro umarnin kamawa tare da gurfanar da duk wata ƙungiya a gaban kotu musamman ga waɗanda ba  a basu izini a hukumance ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: