Aƙalla mutane bakwai ne su ka mutu a sakamakon hatsarin mota da ya faru a ƙaramar hukumar Lavun ta jihar Neja.

 

Hatsarin day a haɗa da mota ƙirar tirela da kuma wata motar ɗaukar fasinja ya faru da misalign ƙarfe 8:48 na daren Lahadi wayewar Litinin.

 

Kwamandan hukumar kiyaye afkuwar haɗɗura ta ƙasa reshen jihar Neja Kumat Tsukwam yatabbatar da faruwarlamarin.

 

Ya ce hatsarin ya faru ne a sanadin gudun wuce sa’a wanda hakan ya sa direban ya kara sarrafa motar don kare afkuwar hakan.

 

Yayin da lamarin ya far shida daga ciki sun mutu nan take yayin da gudaya mutu ranar Litinin a babban asibitin Kutigi na jihar.

 

Tuni su ka miƙa gawarwakin mutanen ga mataimakin shugaban ƙungiyar direbobi da sufuri ta ƙasa reshen jihar.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: