Har yanzu al’umma na ci gaba da kokawa a kan ƙarancin sabbin kuɗi da aka sauyawa fasali.

Da yawan jama’a na yin dandazo a ƙofar bankuna da wajen injinan cirar kuɗi na bankuna wato ATM domin cire kuɗin da za su yi amfani das u yau da kullum.


Wasu bankuna a jihar Kano na bayar da sabbin kuɗin na naira dubu ɗaya kuma iyaka naira dubu goma ga duk wanda zai cira idan ba a bankinsa ba ne.
A dukkanin naira dubu guda da mutum zai cire ana cire haraji wanda wasu ke zargin bankunan sun yi haka ne da nufin ƙara hanyoyin kuɗin shiga.
A gefe guda kuwa gwamnan babban bankin Najeriya CBN Godwin Emefiele ya sake tababbatar da cewar bankin na kan bakansa na daina arɓar tsaffin kuɗin da aka sauya.
Bankin y ace har yanzu ranar 10 ga watan Fabrairu ita ce rana ta ƙarshe da wa’adin karɓar ya ƙare.
Hakan ya sa bankunan ƴan kasuwa su ka dakatar dakarɓar tsaffin kuɗin kuma da yawan mutane ke damuwa a kan hakan.
Mun ji tab akin wasu mutane a kan wannan ƙudiri da babban bankin ƙasa ya sake jaddadawa a yau ga kuma abinda su ke cewa.
Tun a baya bankin ya saka wa’adin ranar 31 ga watan Janairun day a gabata a matsayin ranar ƙarshe da za a daina karɓar tsaffin kuɗi.
Sai dai bankin ya tsawaita lokacin bayan koke da ɗaiɗaikun mutane da ƙungiyoyi su ka yi a kan lamarin.