Jami’an ƴan sanda a jihar Ondo sun mamaye helkwatar babban bankin Njeriya CBN reshen jihar bayan da wasu fusatattun matasa su ka yi yunƙurin nuna fushinsu.

Mutanen da mafi yawansu kwastomomin bankin ƴankasuwa ne sun fusata tare da mamaye babban bankin CBN a Akure bayan ƙin karɓar tsofaffin kuɗi.
A safiyar yau Talata mutanen su ka ce bankunan ƴan kasuwa bas a karɓar tsofaffin takardun kuɗi da aka sauyawa fasali.

Mutanen sun yi ƙorafin cewar har kawo yanzu wasu injinan cirar kuɗi na bankunan ƴan kasuwa na bayar da tsofaffin kuɗi.

A sakamakon haka wasu daga cikin fusatattun matasa su ka lalata wasu bankuna da ke yankin Alagbaka ta jihar.
Sai dai wani guda cikin ma’aikatan CBN a jihar ya shaida cewar, bad a jimawa ba za a bai wa bankunan umarnin ci gaba da karɓar tsofaffin kuɗidaga hannun jama’a.