Mai magana da yawun Kungiyar Dattawan Arewa (NEF), Hakeem Baba-Ahmed, ya siffata sauyin fasalin Naira a matsayin babban matakin rushewar jam’iyyar APC.

Ahmed ya fadi hakan ne wannan Talatar yayin zantawa da Channels TV.
Inda ya ce, mambobin NEF din ya ce shugabancin a makwanni biyu da suka shude yayi nasarar tarwatsa bangeren tattalin arziki da karancin Naira.

A cewarsa, matsin rayuwar da dokar ta jawo na kokarin sawarwaro jam’iyya mai mulki kasa warwas a yankin arewacin Najeriya.

Ya kara da cewa, bai dace a ce babban abokin adawar APC ya dauki babban matakin rushewar jam’iyya mai mulkin ba.
Alamu na nuna shugaban kasa Muhammadu Buhari baya sauraron kowa duk da zai iya kawo karshen matsalar ta hanyar barin amfani da sabbi da tsoffin kudin gaba daya.