Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai tafi birnin Addis Ababa n aƙasar Ethiopia domin halartar taron ƙasashen Afrika.

A wata sanarwar da mai magana da yawunsa Malam Garba Shehu ya fitar, ya ce zai halarci wani taro na musamman yayin ziyarar.

A taron majalisar ƙasashen Afrika za a duba batun kasuwancin bai ɗaya na ƙasashen Afrika.

Sannan kuma zai halarci wani taro da za aa tattauna matsalar tsaro da sauyin yanaayi da kuma siyasa musammna a ƙasashen ta yamma.

Tafiyar za ta samu rakiyar wasu daga cikin ministocin gwamnatinsa da wasu daga muƙarraban gwamnati.

A na sa ran shugaba Buhari zai koma Abuja a raanar 20 ga watan Fabrairu da mu ke ciki.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: