Hukumomi sun tabbatar da cewar zuwa yanzu mutane 40,000 ne su ka mutu sakamakon girgizar ƙasa a ƙasashen Syria da Turkiyya.

Ofishin jin ƙai na majalisar Dinkin Duniya ya tabbaatar da cewar a ƙasar Turkiyya an samu asarar rayuka 35,418 sai mutane 5,814 da su ka mutu a Syria.


A ranar 6 ga waatan Fabrairu aka samu ibtilain girgizar ƙasa a ƙasashen biyu.
Ministan iyali na ƙasar Turkiyya Derya Yenik ya ce a halin yanzu akwai yara 1,362 da su ka rasa iyayensu.
Sai wasu 369 da aka samu iyayensu, sannan akwai yara 792 da ke asibiti sannan wasu 201 da ke ƙarƙashin kulawarsu.
Tun bayan faruwar lamarin, hukumomi ke kira don ganin na tallafawa waɗanda su ka raasa muhallinsu sanadin tsananin sanyi da su ke fama da shi.