Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El’Rufa’i ya bayyana cewa za a ci gaba da karbar tsofaffin kudade a Jihar sa.

El’Rufa’i ya bayyana hakan ne ta cikin wani jawabi da yayi a ranar Alhamis, inda ya ce mazauna Jiharsa za su ci gaba da karbar tsofaffin kudade har zuwa ranar da kotun koli za ta yanke hukunci akan shari’ar da su ka shigar gabanta.

Gwaman El’Rufa’i ya bukaci al’ummar Jihar sa da su ci gaba da amfani da tsoffin kudade ba tare da wani tsoro ba.

El’Rufa’i ya ce hukumomi a Jihar za su dauki mataki akan dukkan wanda ya ki karbar tsohon kudin tare da yi masa hukunci.

Ya kara da cewa kara wa’adin karbar naira 200 da shugaban kasa Buhari ba tare da hadawa da naira 500 da 1000 ba hakan rashin biyayya ne ga kotun Koli.

El’Rufa’i ya ce kafin bayyana sanar da karin karbar naira 200 sai da gwamnatin ta tarayya ta fara gabatar wa da gwamnatotin Jihohi kudurin kara wa’adin karbar naira 200 inda su ka ki amincewa da tayin.

Gwamnan ya bayyana hakan bayan da shugaban kasa Muhamad Buhari ya bayar da umarnin ci gaba da karbar naira 200 daga cikin tsofaffin kudaden da aka sauyawa fasali da kuma daina karbar naira 500 da kuma 1000.

Leave a Reply

%d bloggers like this: