Jami’an hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta gano wani yunkuri da mayakan kungiyar boko haram su ke yi na sake kai wa jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja harin nan ba da dadewa ba.

Hakan na kunshe ne ta cikin wata wasika da Ma’aikatar sufuri ta Tarayya ta aikewa da ma’aikatar domin ta dauki mataki akan yunkurin kai harin.

Ma’aikatar sufurin ta aikewa da hukumar ta DSS wasikar ne tun a ranar 1 ga watan Fabrairun da mu ke ciki.

Ma’aikatar ta sufurin ta bukaci da ma’aikatar tsaro da ta dakile yunkurin kai harin da muhimmanci tare da gudanar da taron masu ruwa da tsaki domin lalubo hanyar da za a dakile harin.

Yunkurin kai harin na zuwa ne kasa da wata daya bayan dawowa da ci gaba da gudanar da sufurin jiragen Kasa na Kaduna zuwa Abuja bayan harin bom da wasu ‘yan bindiga su ka kai masa wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar mutane da dama da kuma yin garkuwa da wasu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: