Wasu matan mutum daya su hudu da ke zaune a sansanin ‘yan gudun hijira da ke Jihar Borno sun haihu rana guda.

 

Kwamishiniyar mata a Jihar Hajiya Zuwaira Gambo ce ta tabbatar da hakan a lokacin da ta ke gabatar da koke a gaban kwamitin da ke gudanar da binciken kan take hakkin Dan-adam a yankunan yaki da ta adda’anci a yankin arewa maso gabas.

 

Hajiya Zuwaira ta ce kawo yanzu ana ci gaba da samun masu juna biyu tare da hayayyafa a sansanonin gyaran hali na boko haram.

 

Kwamishiniyar ta ce ma’aikatar ce za ta dauki nauyin matan da su ka haihu.

 

Hajiya Zuwaira Gambo ta bayyana alhinin ta dangane da yadda ake ci gaba da samun masu juna biyu a sansanoni da kuma haihuwar jarirai duk bayan watanni hudu.

 

Kwamitin bisa jagorancin mai shari’a Abdu Aboki Mai murabus ya bayyana cewa su na ci gaba da gudanar da bincike a kan zargin tilastawa masu juna biyu kusan 10,000 zubar da ciki da kuma neman bayani daga kwamishinar.

 

Hajiya Zuwaira ta musanta zargin,tare da nuna rajin jindadi da rahotannin da ake yadawa wanda bashi da tushe balle makama.

Leave a Reply

%d bloggers like this: