Wasu mutane uku sun rasa rayukan su a lokacin da su ka fada rijiya a lokacin da su ke tsaka da aikin gini a Jihar Osun.

Lamarin ya farune a ranar Juma’a a lokacin da su ke kokarin ciro wani bokiti da ya fada a cikin rijiyar.


Wani mazaunin yankin Alaro Onigbo ya bayyana cewa botikin da ya fada mutanen su na aikin debo ruwa a cikin rijiyar ,wanda hakan ya sanya daya daga cikin su ya shiga daga bisani ya makale a ciki wanda hakan ya sanya ragowar su ka shiga domin su ceto shi su ma su ka makale.
Bayan faruwar lamarin mazauna yankin su ka kira jami’an hukumar kashe gobara inda su ka dauko mutanen.
Mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta Jihar Ibrahim Adekunle shine ya tabbatar da faruwar lamarin ga Jaridar Punch a yau Asabar.
Adekunle ya ce bayan ciro mutane an kaisu Asibiti inda likitocin su ka tabbatar da mutuwar su.