Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC ta lalata magungunan jabu da wasu kayayyaki wanda kudinsu ya kai fiye da naira miliyan 300 a Jihar Nasarawa.

Hukumar ta bayyana hakan ne shafin ta Twitter inda ta ce hukumar ta gano magungunan ne a wasu shaguna da ke Jihar.
Bayan kammala aiki lalata magungunan babbar Darakta a hukumar Farfesa Moji Adeyeye ya ce sayar da magungunan ga ‘yan Najeriya ka iya haifar da babbar cuta a garesu.

Adeyeye wanda ya samu wakilcin daraktan bincike na hukumar ya bayyana cewa an kwato magungunan ne daga wasu kamfanoni da shaguna da ke samar da su.

Moji ya bayyana cewa sun lalata magungunan ne domin kare lafiyar al’ummar Jihar da ma kasa baki daya.