Rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara ta kama wani matashi mai shekaru 20 sakamakon zargin sa da hada baki da wasu mutane biyar su ka yi garkuwa da mahaifiyar sa da wasu mutane uku hadi da karbar kudin fansa naira miliyan 30.

 

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Jihar SP Muhammad Shehu shi ne ya tabbatar da hakan a ranar Juma’a a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a Gusau babban birnin Jihar.

 

SP Shehu ya ce matashin ya shaida musu cewar bayan yin garkuwa da mutanen sun karbi naira miliyan goma daga kowanne yayin da su ka karbi naira miliyan 30 a matsayin kudin fansar mahaifiyar sa.

 

Kakakin ya kara da cewa sun kama mutanen ne da taimakon bayannan sirri da su ka samu daga jami’in su inda su ka binciko maboyar batagarin tare da kama shida daga cikin su.

 

Muhammad Shehu ya ce wadanda aka kama sun addabi kauyuka da dama a Jihar Kaduna da Kano Sokoto da kuma wasu Jihohi da ke makwabtaka da Jihar.

 

Shehu ya bayyana cewa bayan binciken da su ka gudanar sun gano cewa wadanda ake zargin sun dade su na garkuwa da mutane da kuma karbar miliyoyin kudade a matsayin kudin fansa.

 

Kazalika ya ce kowanne sun ya bayyana musu yadda ya kware a gurin fansar mutane tare da irin ayyukan da yake gudanarwa.

 

Kakakin ya tabbatar da cewa bayan sun kammala bincike za su gurfanar da su a gaban kotu domin yi masa hukunci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: