Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya gargadi ga masu harkar kasuwancin banki a jihar Kano da ba sa yarda su karbi tsofaffin kudin da aka canza.

 

Channels TV ta rahoto Dr. Abdullahi Umar Ganduje yana barazanar rusa bankunan da ba su amincewa su yi kasuwanci da tsofaffin N500 da 1000.

 

Gwamnan ya yi wannan bayani ne a lokacin da yake duba kayan abincin da za a rabawa al’umma saboda radadin rayuwar da ake fama da shi.

 

Da yake bayani a ranar Juma’ar da ta gabata, Gwamnan ya ce ba zai amince bankuna su rika yi wa umarnin kotun karon tsaye a kan batun canjin kudi ba.

 

Gwamnan ya ce rahoto Gwamna Abdullahi Ganduje ya ce Najeriya ba mallakin gwamnan babban banki, Godwin Emefiele ba ce.

 

Gwamnan yake cewa duk bankin da bai amfani da kudin da aka sauya, zai jawo al’umma su yi asara kenan, ya nuna ba za su yarda da haka a Kano ba.

 

Dr. Ganduje ya kafa kwamiti da zai sa ido, kuma ya bukaci mutane su kawo karar bankin da ya saba domin a karbe masa lasisi, sannan a ruguza gininsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: